Jamus na tanadin dokoki bayan Brexit
January 18, 2019Talla
Sabuwar dokar ta samu amannar kusan yawancin wakilan jam'iyyun siyasa a majalisar dokokin Bundestag in ban da jam'iyyar AfD, za ta ba wa 'yan Birtaniya mazauna Jamus kusan dubu 120 damar neman izinin zama 'yan kasa kamin kammala shirin ficewra Birtaniya daga EU nan da 2020. Jamusawa da ke son izinin zama 'yan Birtaniya na da damar cimma burinsu kamin kammala shirin Brexit, sai dai ba kasafai dokokin Jamus ke ba da damar mallakar izinin zama dan kasashe biyu ba.