1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na tunawa da gama yakin duniya na 2

May 8, 2022

A wannan Lahadin ce Jamus ke bikin tunawa da cika shekaru 77 da gama yakin duniya na biyu. Mutane sun yi jerin gwano a birnin Berlin.

Berlin | Gedenken an das Endes zweiten Weltkrieg - Ukrainische Flagge
Hoto: Markus Schreiber/AP/picture alliance

A birnin Berlin da ke zama fadar gwamnatin Jamus, mutane da dama sun yi jerin gwano a wuraren tunawa da tarihi, sai dai kuma an jibge jami'an 'yan sandan don kaucewa barkewar rikici saboda mamayar da Rasha ta kaddamar a Ukraine.

A lokacin da yake jawabi a birnin Berlin, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce wannan rana ta dade da kasancewa ranar da ake da babban fata sai dai ta bana bata zo da hakan ba, ya na mai alakanta ta da yakin da ke tsakanin Rasha da Ukraine. 

Ana nashi jawabin ga 'yan kasa, shugaba gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kara jadadda goyon bayansa ga Ukraine, ya na mai nuna yakinin cewa Putin ba zai samu nasara a yakin ba.