1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalantar harkokin tsaro a Turai

Binta Aliyu Zurmi
February 18, 2022

Jamus ta zargi Rasha da yunkurin tada zauna tsaye a kasashen Turai da wasu bukatu da suka ce na musu tuni da lokacin yakin cacar baka a rikicinta da kasar Ukraine.

Außenministerin Baerbock in Jordanien
Hoto: picture alliance/dpa

A daidai lokacin da shugabannin kasashen yamma ke fara wani taron tsaro na shekara shekara a birnin Munich na kasar Jamus a yau, ana ci gaba da fargabar yiwuwar Rasha ta mamaye Ukraine.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta ce akwai bukatar Rasha ta nuna da gaske take wajen kawo karshen wannan takaddamar da aka kwashe lokaci ana yi. Ta kara da cewar Rasha na kalubalantar ka'idojin zaman lafiya na kasashen Turai.

Rikicin Rasha da Ukraine dai shi ne babban batun da zai mamye zauren taron tsaro na Munich, sai dai Rasha ta janye kanta daga halarta taron abin da ministar harkokin wajen Jamus din ta ce bai kamata ba.