1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Samame kan masu fasa kwaurin mutane

Zainab Mohammed Abubakar
November 23, 2023

'Yan sandan Jamus sun cafke wasu mutane biyu, a wani samame kan wasu masu shirya fasa kwaurin bakin haure a fadar mulkin kasar kasar Berlin da jihar Lower Saxony da ke arewaci.

Deutschland, Berlin | Razzia im Zusammenhang mit dem Verbot der Hamas und von Samidoun
Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Kimanin jami'ai 260 ne suka kai samamen da bincike a wurare takwas a Lower Saxony da kuma wasu shida a Berlin. Ana zargin mutanen biyu da yin safarar bakin haure sama da 200, yawancinsu 'yan kasar Siriya zuwa cikin  kasashen Tarayyar Turai, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Jamus dpa ya ruwaito.

An kama daya daga cikin wadanda ake zargin, dan shekaru 23 daga Berlin, a garin Garbsen kusa da Hannover. Dayan kuma, mai shekaru 40, na tsare ne a kusa da Hanover, bisa warantin kamunsa na kasar Austriya da ke makwabtaka.

Hukumomi ba su bayyana sunayen mutanen da ake zargin ba. Amma jami'an tsaro sun yi zargin cewa mutanen biyun na cikin gungun masu fasa kwaurin bakin haure, yawancinsu 'yan Iraki, wadanda ake zargin sun shigo da akalla baki 208 zuwa cikin EU ta barauniyar hanya, yayin gomman tafiye-tafiye tsakanin Agusta 2022 da Yuni 2023.