Jamus: Saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa
November 20, 2018Talla
An fara binciken lamarin ne bayan da jami'an tsaro suka gano gawar mutane ukun a gabashin birnin Jena, sai dai ba a tabbatar da musababbin abin da ya sa shi aikata kisan ba, amma hukumomi na ci gaba da binciken lamarin.
Wannan dai na zuwa ne a daidai loakcin da hukumomin Jamus ke shirin bayyana sabbin alkaluman kisa ta hanyar cin zarafi a fadin kasar baki daya, inda a shekara ta 2016 alkaluma sun nuna cewa mutane 147 ne aka kashe ta hanyar cin zarafi ko kisa da wuka.