1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Schulz zai kalubalanci Merkel

Ahmed Salisu RGB
June 26, 2017

Jam'iyyar SPD da ke kan gaba wajen kalubalantar jam'iyya mai mulki a nan Jamus ta gudanar da babban taronta inda ta amince da Martin Schulz a hukumance a matsayin dan takararta.

Deutschland SPD Programmparteitag in Dortmund | Martin Schulz
Hoto: Reuters/W. Rattay

Taron wanda ya gudana a birnin Dortmund na jihar North Rhine Westphalia a jiya Lahadi ya duba batutuwa da dama ciki kuwa har da sabbin manufofin jam'iyyar ta SPD da ma shirye-shiryen da za su yi amfani da su wajen tallar dan takararsu wato Martin Schulz a zaben gama-gari da ke tafe wanda mambobin jam'iyyar suka amince da shi ba tare da an kai ruwa rana ba. Hakan dai yanzu na nufin cewar Schulz ne a hukumance zai kalubalanci Angela Merkel a wajen neman kujerar shugaban gwamnati.

Daga cikin batutuwan da jam'iyyar ta fi maida hankali a kai su ne batun kasancewar Turai tsintsiya madaurinki daya da yin adalci ga kowa musamman mata da ma magana ta ganin cewar al'umma sun kasance cikin yanayi na walwala kamar dai yadda Mr. Schulz din ya bayyana lokacin da aka gabatar da shi ga 'ya'yan jam'iyyar ta SPD a wajen taron yana mai cewa.

CDU ta Angela Merkel ta musanta zargin da ake mata na rashin manufofi na gari da za su yi amfani da su wajen tallata jam'iyyarHoto: Reuters/F. Bimmer

Baya ga wannan, a jawabin na Schulz na mintuna 80 ya tabo batu na inganta ilimi kama daga firamare ya zuwa jami'a da kuma habakar jam'iyyu masu kyamar baki. A share guda Schulz ya caccaki abokiyar hammayarsa wato Angela Merkel ta jam'iyyar CDU da ke mulki inda ya ce jam'iyyarta ta gaza yi wa 'yan kasar  cikakkaken bayani game da inda ta sa gaba kana ta gaza wajen fidda manufofinta gabannin zaben da ke tafe, wannan inji Schulz karan tsaye ne ga demokradiyya.

To sai dai jam'iyyar CDU ta Merkel ta ce wannan zance Schulz ya ke yi ba abin kamawa ba ne kasancewa suna da shirye-shiryensu na musamman wanda talaka zai amfana da su kamar yadda sakataren jam'iyyar CDU Peter Tauber ya shaidawa manema labarai. Tauber ya ce kalaman Schulz kalamai ne na wanda alamu suka nuna cewar zai sha kaye a zabe, inda a share guda ya bukaci da jam'iyyar ta SPD da ma Schulz din su rika tauna magana kafin su yi ta.

Gerhard Schröder ya ce abinda ke gaban jam'iyyarsu baya ga karbe madafun iko shi ne tabbatar da SPD a matsayin jam'iyya mai karfin gaskeHoto: Reuters/W. Rattay

A daura da wannan batu, Gerhard Schroeder da ke zaman tsohon shugaban gwamnatin Jamus kana jigo a jam'iyyar ta SPD da ke adawa ya ce ''za mu yi kokari wajen hade karfinmu waje guda a makonnin da ke tafe wajen ganin mun samu kuri'u da nufin ganin mafarkinmu ya tabbata kuma ina da yakinin cewar jam'iyyarmu ta SPD za ta kasance mai karfin gaske a fagen siyasar Jamus''

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani