1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi jawabin shekara

December 31, 2020

Angela Merkel ta gudanar da jawabin ta na sabuwar shekara kuma na karshe a matsiyin shugabar gwamnatin Jamus.

Angela Markel in Berlin 22.10.2014 Symbolbild USA Deutschland Beziehungen
Hoto: Getty Images/AFP/Odd Andersen

A cikin wani yanayi mai kama da na alhini, uwar gida Angela Merkel ta gudanar da jawabin ta na sabuwar shekara kuma na karshe ga 'yan kasar a matsayinta na shugabar gwamnatin Jamus. Merkel ta ce a tsawon jagorancinta na shekaru kusan goma sha biyar, babu shekarar da ta fi fuskantar kalubale kamar wannan ta 2020 da muke bankwana da ita. Barkewar annobar Corona ta tsaurara al'amurra, amma tare da taimakon rigakafin da aka samu lamurra za su inganta a shekara mai zuwa ta 2021 a cewar ta. Nan da watanni tara ne za a gudanar da zabukan 'yan majalissu a kasar ta Jamus, wanda Markel din ta ce ba za ta kara tsayawa takara ba.