Jamus: Shiga kawancen tsaro a tekun fasha
July 28, 2019Jamus na duba yiwuwar bin sahun sauran kasashen Turai wajen tabbatar da tsaro akan tekun fasha. Tsohon jakadan Jamus a Amirka Wolfgang Ischinger wanda a yanzu yake shugabantar babban taro kan al'amuran tsaro na Munich ya sanar da hakan a wannan Lahadi.
A halin da ake ciki dai ana takaddama tsakanin Iran da Birtaniya kan 'yancin jigila inda kasashen biyu suka kwace jiragen dakon mai a yankin.
A ranar Litinin da ta gabata Birtaniya ta bada shawarar kafa wata rundunar sojin ruwa na tarayyar Turai domin bada kariya ga jiragen ruwan da ke wucewa akan tekun fasha.
Ischinger yace martabar Jamus ce ta bada gudunmawa a wannan fanni na jigilar jiragen ruwan kasa da kasa musamman ta la'akari da matsayin Jamus na safarar kayayyaki zuwa kasashen waje.
A makon da ya gabata ma ministar tsaron jamus Annegret Kramp Karrenbauer ta hannun ministan harkokin waje Heiko Maas ta nuna yiwuwar shigar kasar cikin tawagar sojin ruwa na tarayyar Turai a gabar ruwan Iran.
Sai dai ta ce Jamus din na bukatar sanin ko rundunar za ta kasance ne karkashin kungiyar tarayyar Turai EU ko Majalisar Dinkin Duniya ko kuma wata kungiya ta kasa da kasa da kuma ko jiragen ruwan za su kasance cikin shirin yaki.