1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Shirin bunkasa rundunar sojoji da matasa

November 13, 2025

Gwamnatin Jamus ta cimma yarjejeniyar kara yawan sojojinta da matasa 'yan shekaru 18 da ke muradin aikin soji.

Deutschland Berlin 2025 | Bundeswehr-Zeremonie vor Schloss Bellevue I Wehrpflicht Symbolbild
Hoto: Malin Wunderlich/dpa/picture alliance

Wannan mataki a cewar gwamnati, zai taimaka wajen gano wadanda suka dace da aikin soja da kuma jawo hankalin sabbin ma’aikata cikin rundunar. Bayan watanni na doguwar tattaunawa tsakanin jam’iyyun hadin gwiwa na CDU da SPD, gwamnatin Jamus ta sanar da sabon tsari na karfafa rundunar sojanta.

Sabon tsarin da aka amince da shi zai hada da aika takardun tambayoyi ga duk matasan da suka kai shekaru goma sha takwas a badi. Tambayoyin za su shafi sha’awarsu da kuma cancantarsu wajen shiga aikin soja. Sai dai gwamnati ta ce ga maza, amsa tambayoyin wajibi ce, abin da ya sa wasu ke ganin zai iya zama wata hanya ta sake dawo da tsarin tilasta aikin soja da aka soke tun shekarar 2011 Ministan Tsaron Jamus, Boris Pistorius, ya bayyana cewa wannan yunkuri ne na zama a cikin shiri:

Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

"Abin da muke so mu cimma shi ne mu zama a shirye muke sannan mu samu yawan matasa a cikin aikin. Sannan abu na biyu shi ne duk kasashen duniya suna ganin yadda mu ke yi sannan muna tattaunawa da shuwagabannin kasashen duniya kamar su Burtaniya.

A cewar gwamnatin, wannan sabon shiri na daga cikin matakan da za su taimaka wajen kara yawan sojojin kasar daga sojoji dubu 180  zuwa  dubu 260 cikin ‘yan shekaru masu zuwa. Yunkurin da ake ganin zai karfafa garkuwar kasar dan fuskantar barazanar Rasha.

Duk da yake akwai masu goyon baya ga wannan mataki, ra’ayoyin ‘yan kasar sun kasu kashi biyu. Wani binciken ra’ayin jama’a da kamfanin YouGov ya wallafa a watan Yunin 2025 ya nuna cewa a tsakanin matasa  masu shekaru 18 zuwa 29, goyon bayan tsarin ya ragu zuwa kashi 35 cikin 100.

Ministan Tsaron Jamus, Boris Pistorius ya kara da cewar shirin kan iya zama abin koyi ga wasu kasashen Turai:

"Wannan tsarin da muka fitar sabon tsari ne da muke ganin kan iya zama abin koyi ga wasu kasashen."

Hoto: Hauke-Christian Dittrich/dpa/picture alliance

Gwamnatin ta kuma ce idan har ba a samu isassun matasan da suka nuna sha’awar shiga aikin soja ba daga cikin wadanda aka tattara bayanansu, to za a iya daukar matakin tilasta musu shiga daga karshe.

Wannan ba shi ne karo na farko da gwamnatin Jamus ta yi yunkurin kara yawan sojojinta ba. Sai dai a yanzu, gwamnatin na ganin sabon tsarin na tattara bayanai daga matasa na iya zama hanya mafi inganci ta karfafa tsaro da karfin sojan kasa.