Jamus: Zargin 'yan majalisa da rashawa
January 30, 2020Talla
Masu shigar da kara a birnin Frankfurt sun ce, wajen jami'an 'yan sanda 100 ne suka gudanar da wannan somame daban daban a kan 'yar majalisa Karin Strenz da tsohon dan majalisa Eduard Lintner na jam'iyyar tagwaitakar CDU watau CSU da ke Bavaria.
A yayin somamen, an gudanar da bincike a jihohin tarayya na Mecklenburg-Western Pomerania da Bavaria, da Berlin da kuma kasar Beljium bayan cirewa Strenz rigar kariya ta majalisa da safiyar yau Alhamis.
Ana zargin 'yan siyasar biyu da laifin karbar kudi da yawansu yakai euro dubu 22, domin neman alfarma wa gwamnatin Azerbaijan a majalisar Turai.