1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Jamus ta amince da daga wa Girka kafa

Lateefa Mustapha Ja'afarFebruary 27, 2015

Sai dai masu ra'ayin rikau na jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na nuna adawarsu da wannan karin wa'adi.

Deutschland Bundestag Debatte Griechenland Hilfe Abstimmung
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Majalisar dokokin kasar Jamus ta amince da daga wa kasar Girka kafa da aka yi har na tsahon watanni hudu kafin ta biya bausussukan da ake binta wanda aka tallafa mata dashi a kokarin ceto kasar daga durkushewa.

Wakilai 541 daga cikin 586 na majalisar dokokin kasar ta Jamus ne suka amince da a daga wa kasar ta Girka kafa da watanni hudu domin ta biya bashin da kasashen da ke amfani da kudin Euro wato Eurozone suka bata a baya domin ceto ta daga durkushewa. Daga cikin 'yan majalisa 32 da suka hau kujerar na ki 29 'yan jam'iyyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta CDU ne da kuma kawarta jam'iyyar CSU. Rahotanni sun nunar da cewa a ranar Asabar ne wa'adin farko da ya kamata kasar ta Girka ta biya bashin da ake bin nata ke cika, sai dai a yanzu za ta biya bashin ne a karshen watan Juni mai zuwa. Acewar ministan harkokin kudi na nan Jamus Wolfgang Schaeuble Girkan za ta kammala tanade-tanaden da ake bukata a karkashin tsarin ceton kasar wanda aka kara wa'adin biyan sa zuwa watan Yuni mai zuwa. Ya kara da cewa ba wai an sauya tanade-tanaden ba ne a'a, an dai kara tsawaita lokacin biyan bashin ne.

Hoto: Reuters/H. Hanschke

Sai dai duk da haka wasu 'yan majalisar na ganin cewa bai kyautu a daga wa kasar ta Girka kafa ba kamar yadda daya daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar ta Jamus daga jam'iyyar CSU Hans Michelbach ke cewa ba a yi wa sauran kasashen da ake bi bashi ba haka.

"Dole ne a duk matakin da zamu dauka mu yi wa sauran kasashen da aka baiwa bashi domin cetonsu adalci. Kamar Potugal da Spain da Irland. Suma za mu iya daukar irin matakin da muka dauka a kan Girka. Suma kasashen za su iya kwaikwayon abunda Girka ta yi. A ganina yana da amfani mutum ya fadi abunda ke zuciyarsa".

A jawabinsa Firaministan kasar ta Girka Alexis Tsipras ya sha alwashin fara yin aiki tukuru domin kawo gyara mai amfani ga kasar yana mai cewa Jamus ta kada kuri'ar bada tabbaci ga kasashen nahiyar Turai.