1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta samar da daftarin dokar corona

Ramatu Garba Baba
April 22, 2021

Shugaba Frank-Walter Steinmeier ya rattaba hannu kan doka da za ta bayar da damar daukar matakan bai daya domin dakile cutar corona a wuraren da annobar ke yaduwa cikin gaggawa.

Berlin Konzerthaus am Gendarmenmarkt | Rede Steinmeier | Gedenkfeier Covid-Opfer
Hoto: Michael Sohn/AFP/Getty Images

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya rattaba hannun kan sabuwar dokar da za ta bai wa gwamnatin kasar damar aiwatar da dokar hana yaduwar annobar corona. Amincewa da dokar a hukumance, na nufin dokar za ta yi aiki a dukkan wuraren da ake samun yaduwar annobar a jihohi 16 na tarayyar kasar

A dai jiya Laraba,  'yan majalisar dokokin Jamus, suka kada kuri'a kan daftarin shawarwari da Shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar, wanda zai tilasta daukar matakin na bai daya, domin dakile cutar corona a wuraren da annobar ke yaduwa cikin gaggawa, dokar za ta cigaba da aiki har zuwa karshen watan Yuni. Dubban masu adawa da daftarin yaki da coronar na ci gaba da baiyana adawarsu, inda suka ce matakin ya ci karo da 'yancin dan Adam.