1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta amince da girke makaman nukiliya na Amirka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 21, 2024

Jamus ta amince da shirin girke makaman nukiliya na Amirtka a kasarta saboda samun kariya daga barazanar Rasha

Hoto: dpa

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, ta nuna goyon bayan kasarta ga shirin amfani da kasar a matsayin sansanin girke makaman nukiliya masu linzami da ke cin dogon zango kirar Amurka, don dakile duk wata barazana daga Rasha.

Karin bayani:Ko Jamus za ta iya jagorancin NATO a Turai?

Kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito cewa ministar harkokin wajen ta Jamus ta  bayyana hakan a zantawarta da jaridar Funke Media ta wannan Lahadi, tana mai jaddada cewa hakan ya zama wajibi sakamakon yadda shugaban Rasha Vladimir Putin ke kara fadada ikonsa, wanda ke zama barazana ga 'yancin nahiyar Turai.

Karin bayani:NATO za ta bai wa Ukraine karin makaman kakkabo jiragen yaki na sama

Ko da yake wannan shiri na gwamnatin hadakar jam'iyyu uku na fuskantar suka daga cikin gida, la'akari da korafin da Rolf Mützenich, jigon jam'iyyar SPD ta shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi, kan hatsarin da ke tattare da wannan mataki.