1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta amince da 'yancin kan Kosovo

Abdullahi Tanko BalaFebruary 20, 2008

Serbia ta janye jakadunta daga ƙasashen turai da suka amince da Kosovo

Ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter SteinmeierHoto: picture-alliance/ dpa


A yau ne gwamnatin tarayyar Jamus ta sanar da amincewa da lardin Kosovo a matsayin 'yantacciyar ƙasa mai cin gashin kanta,kuma nan bada jimawa ba zata buɗe ofishin jakadancin ta a wannan ƙasa

Kakakin gwamnatin tarayyar ta Jamus Ulrich Wilhelm,ya bayyana hakan,yace zasu sauya ofishin hulɗa da jama'a da jamus ɗin keda shi a Pristina zuwa cikakken ofishin jakadanci.

Yanzu haka dai ministan harkokin tsaro na Jamus Franz Josef Jung ya na kan hanyar sa zuwa Kosovo domin tattaunawa da shugaba Fatmir Sejdiu da Primiya Hashim Thaci da Commandan rundunar tsaro ta NATO dake yankin.

Jamus dai na mai zama babbar ƙasar turai ta uku bayan Britania da Faransa da ta amince da Kosovo,bayan ta ayyana 'yancin kan ta a ranar lahadi.

Serbia dai ta mayar ta martaninta ta wata sanarwa da ministan harkokin wajen ta Vuk Jeremic ya gabatar a Strasbourg,wanda ke nuni dacewar zata janye jakadun ta daga Jamus da Austria ,ƙasar da ita ma ta amana da Pristina a matsayin kasa mai zaman kanta.

"Mun janye jakadanmu daga kasar Faransa jiya kuma ayau zamu janye na ƙasashen Austria da Jamus.Duk ranar da Italiya ta sanr da amincewar ta, ranar ce zamu janye jakadan mu daga birnin Rome"

Jeremic yace Serbia zatayi amfani da matakai na diplomasiyya da wasu hanyoyi da suka cancanta na kaida,wajen dakatar manufofin na Kosovo,wanda ta dangana da kabilanci,kasancewar hakan ya saɓawa democraɗiyyan su.

Jamus dai tace kawo yanzu ba a shaida mata a hukuman ce cewar Serbia zata janye jakadanda daga Berlin ba,kuma akwai shakkun yiwuwar yanke hulɗa da jamus a bangaren ita Belgrade.

Kakakin maaikatar harkokin waje na jamus Martin Jaeger yace ,hakan ya faru akan wasu kasashen turai da suka nuna goyon bayan su dangane da wannan 'yancin na Kosovo,amma ba komai bane face Diplomasiyya.

Yace hakan bawai yana nufin yanke dangantakar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu bane,sai dai kawai matakai na wariya.

Gwamnatin Jamus ɗin dai ta sanar da manufar ta na taimakawa Kosovo a matakan ƙasa da ƙasa wajen zama zaunanniyar ƙasa,kana a hannu guda kuma zata cigaba da taimakawa Serbia dangane da cimma burin ta na haɗewa a ƙungiyar Tarayyar Turai.

Shugabar gwamnati Angela Merkel tayi kira ga Kosovo da Serbia,dasu cigaba da darajawa dokokin ƙasa da ƙasa domin kare makomar dangantakan su nan gaba da ƙasashen Turai.

Ana saran mafi yawa daga cikin ƙasashen na turai dai zasu bada goyon bayan su wa 'yancin kan Kosovon,ayayinda kalilan daga cikin su akarkashin Jagorancin Spain sun nuna adawa,samun 'yancin Lardin zai iya tayar da kayar baya a ɓangare 'yan aware dake nasu ƙasashen.Sai dai acewar Jamus da Britania wannan ba dalili bane.