1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ce Rasha barazana ce ga Turai

Zainab Mohammed Abubakar
June 14, 2023

Jamus ta sanar da dabarun tsaro, inda ta kira Rasha babbar barazana ga Turai da gargadi kan karuwar gogayya da China da ke amfani da karfin tattalin arziki don manufofin siyasa.

Deutschland | Kabinett beschließt Nationale Sicherheitsstrategie
Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Daftarin ya kunshi bayanan manufofin Berlin na ketare, wanda ya mayar da fifiko kan tsaro fiye da muradun tattalin arziki a cikin shekara daya da rabi tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

Da ya ke gabatar da shi, shugaban gwamnati Olaf Scholz ya ce "Wannan babban garon bawul ne da mu ke aiwatarwa a Jamus a game da yadda manufofinmu na tsaro za su kasance, wanda ya kunshi kauracewa dabarun aikin soja kadai zuwa ga hadadden tsarin tsaro.

Daftarin kazalika ta kumayi bayani  kan kama daga barazanar sauyin yanayi zuwa matsalar tsaiko wajen samar da kayayyaki.