1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta ba da karin tallafin miliyoyi ga al'ummar Gaza

September 6, 2024

Yankin Gaza zai samu karin tallafin Euro miliyan 50 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 55, daga Jamus. Ministar harkokin wajen kasar Annalena Baerbock ce ta yi wannan shela a Amman na kasar Jordan.

Ministar Harkokin Wajen Jamus Annalena Baerbock da takwaranta na Jordan Ayman al-Safadi
Ministar Harkokin Wajen Jamus Annalena Baerbock da takwaranta na Jordan Ayman al-SafadiHoto: Soeren Stache/dpa/picture alliance

Annalena Baerbock ta shaida wa takwaranta na Jordan Ayman Al-Safadi cewa, tun daga fara yakin kawo yanzu Jamus ta bawa al'ummar Falasdinawa tallafin sama da Euro miliyan 360. Babbar jami'ar ta kara da cewa an samar da karin tallafin ne domin tunkarar kalubalen abinci da ruwan sha da magunguna da sauran kayan agajin jinkai da mutanen Gaza ke tsananin bukata gabanin shawo kan Isra'ila da Hamas domin su cimma yarjejeniya tsagaita wuta.

Karin bayani:Bukatar dakatar da harin Isra'ila a Falasdinu 

A cewar ofishin ma'aikatar harkokin wajen Jamus, a duk mako manyan motocin dakon kaya na Jamus kimanin 120 na shiga Zirin na Gaza, domin kai kayan agajin gaggawa zuwa yankin daga Jordan, wanda Jamus ke kashe kimanin Euro miliyan biyar wajen jigilar kayayyakin.