1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta samu rigakafin corona daga Jamus

December 3, 2021

Jamus ta sanar da bayar da tallafin alluran rigakafin corona sama da miliyan biyar ga Najeriya. Bayanin hakan na cikin sanarwar da ofishin jakadancin Jamus da ke Najeriya ya aike wa DW Hausa.

G7 Gipfel Schloss Elmau Merkel mit Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/C. Hartmann

Jamus ta ce ta yi nasarar kawo alluran da suka hada da samfurin Johnson & Joshnson  a cikin makonni bakwan da suka gabata.

Tallafin dai ya zo wa Najeriya a karkashin shirin MDD na COVAX da ke bayar da tallafin rigakafin corona ga kasashe masu tasowa. Jakadar Jamus a Najeriya Birgitt Ory ta ce Jamus na a sahun gaba wurin bayar da tallafin rigakafi a shirin na COVAX. Ta ce Jamus ta gamsu cewa sai kowa ya samu rigakafin corona sannan duniya za ta kauce wa hatsarin kamuwa da corona.