Jamus ta bi sahun neman a dakatar da yaki a Sudan
November 1, 2025
Talla
Ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin mummunan bala’i, yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tare a Sudan din.
A taron da aka gudanar a Bahrain, kasashen Burtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo karshen tashin hankalin.
Tun watan Afrilu 2023, dakarun rundunar RSF ke fafatawa da sojojin gwamnati.
A karshen makon da ya gabata, RSF ta kori rundunar soji daga sansanin ta na karshe a yammacin Darfur.
Rahotanni daga garin El-Fasher sun bayyana cewa ana samun kashe-kashe ba tare da shari’a ba, da fyade da fashi da ma hare-hare kan ma’aikatan agaji.