1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta bukaci 'yan kasarta su fice daga Ukraine

February 19, 2022

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta gargadi 'yan kasarta da ke zaune a Ukraine su fice daga kasar tana mai cewa zaman dar-dar da kuma sojoji da Rasha ta jibge a kan iyakar na kara yin kamari.

Ukraine Kiew Vergoldete Zwiebeltürme
Hoto: DW

Zaman tankiya tsakanin Rasha da Ukraine na kara yin kamari sakamakon dubban daruruwan sojoji da Rasha ke jibgewa a kusa da iyakar kasashen byiyu. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta fitar ta ce akwai yiwuwar barkewar yaki a kowane lokaci.

Sanarwar ta shawarci Jamusawan da ke Ukraine su gaggauta ficewa tana mai cewa idan Rasha ta afkawa Ukraine ba za a sami sukunin kai musu dauki cikin hanzari ba.

A waje guda kuma shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bukaci Rasha ta kauce wa fadawa rikici da makwafciyarta Ukraine.

Yayin da yake jawabi a taron tsaro da ke gudana a birnin Munich na nan Jamus, Stoltenberg ta ce har yanzu lokaci bai kure wa Rashar ba ta sauya manufarta na shirin yaki, ta kuma fara shirin samar da zaman lafiya. Ko da yake tun a baya Rashar ta musanta zargin mamaye Ukraine din da ake mata.

A nata jawabin, shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce kungiyar EU a shirye ta ke ta dauki matakin sanya wa taakunkumin karya tattalin arziki idan har ta cimma manufarta na mamayar Ukraine.

Shugabar ta jadadda bukatar kasashen kungiyar su kara yawan hanyoyin samar da makamashi, saboda a cewarta ba za su ci gaba da dogara kan kasar da ke son fara yaki a nahiyarsu ba.