Jamus ta caccaki Donald Trump kan Ukraine
February 24, 2026
Da yake magana da gidan rediyon Deutschlandfunk, Pistorius ya ce matakin ya saryar da wata muhimmiyar dama ta yin tattaunawa mai muhimmanci da Rasha. Haka kuma ya zargi Trump da wuce gona da iri wajen shigewa shugaban Rasha Vladimir Putin, yana mai cewa hakan ya kara wa Putin karfin gwiwa.
Yau ake cika shekaru hudu da yakin Ukraine
Ministan ya kuma ce Amurka ta janye yawancin tallafin soji ga Ukraine, sai dai bangaren musayar bayanan sirri, tare da zargin cewa yanzu Amurkan na sayar da makamai ne da Turai ke shan wahalar shawo kansu.
Ana dab da cika shekaru hudu da farmakin Rasha a Ukraine
Pistorius ya kuma yi Allah-wadai da hare-haren sama da Rasha ke kai wa kan cibiyoyin makamashi na Ukraine, yana mai cewa ana kai farmaki kan fararen hula a yanayin hunturu mai tsanani domin karya musu gwiwa.