Jamus ta ce dole EU ta dauki matakai kan harajin Trump
July 13, 2025
Ministan kudi na Jamus ya ce ya zama wajibi Tarayyar Turai ta dauki kwakkwaran matakai domin tinkarar karin kudin fito na kashi 30% da shugaban Amurka Donald Trump ya labata muddin ba a kai ga samun daidaito a tsakanin bangarorin biyu ba.
Karin bayani: Trump ya amince da jinkirta karin haraji kan kasashen EU
A wata hira da ya yi da jaridar Sueddeutsche Zeitung, ministan kudin Lars Klingbeil ya jaddada bukatar tattaunawa da Amurka domin samun masalaha, amma kuma ya kara da cewa idan hakan ya ci tura Tarayyar Turai na bukatar matakai masu inganci domin kare guraben aiki da masana'antun nahiyar.
Hakazalika Mista Klingbeil ya ce kofofin Tarayyar Turai na ci gaba da kasancewa a bude domin cimma matsaya daidai ruwa daidai tsaki, amma kuma ya yi kashedin cewa kungiyar ba za ta bari a watsa mata kasa a ido ba.
Karin bayani: Trump ya lafta wa EU sabon haraji, von der Leyen ta lashi takobin mayar da martani
A jiya Asabar ne dai shugaba Trump ya sanar da karin harajin na kashin 30% ga EU da kuma Mexico da zai fara daga ranar daya ga watan Oktoba mai zuwa yana mai da'awar cewa kasashen Turai na ci da gumin Amurka a alakar kasuwanci.