1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta ce Iran ta tallafa dakile rikicin Gabas ta Tsakiya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 28, 2024

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ce ta yi wannan kira, yayin tattaunawa da mai rikon mukamin ministan harkokin wajen Iran Ali Bagheri Kani ta wayar tarho

Hoto: Thomas Koehler/photothek/picture alliance

Jamus ta bukaci Iran da ta taimaka wajen dakile rincabewar rikicin Gabas ta Tsakiya, sakamakon halin fargaba da aka shiga la'akari da yadda lamuran tsaron yankin ke kara sukurkucewa.

Karin bayani:Kaucewa ta'azzarar rikicin Gabas ta Tsakiya

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ce ta yi wannan kira, yayin tattaunawa da mai rikon mukamin ministan harkokin wajen Iran Ali Bagheri Kani ta wayar tarho, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Jamus din ta wallafa a shafinta ta na X.

Karin bayani:Jamus ta yi kira ga Isra'ila ta kauce wa take hakkin 'dan adam a Gaza

A Juma'ar nan ce dai al'ummar Iran suka je rumfunan zabe domin kada kuri'ar zaben sabon shugaban kasa, biyo bayan mutuwar shugaba Ebrahim Raisi, sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan Mayun da ya gabata.