Kamfanin Daimler zai janye motoci dubu 774 daga zirga-zirga
June 11, 2018Talla
Hukumomin na Jamus sun ce an yi ha'inci wajen kira motoci da aka yi da algushi wadanda ka iya sakin hayakin da ke gurbata muhali. A jamus kawai kamfanin zai janye motoci dubu 238, to sai dai shugabannin kamfani sun ce za su kawo gyara ga irin kura- kuran da aka samu da ka iya janyo matsalar gurbata muhali.