Jamus ta dakatar da tallafin da take bayar wa ga UNRWA
January 28, 2024![Shugaban hukumar UNRWA, Philippe Lazzarini](https://static.dw.com/image/68105021_800.webp)
Hakan dai na zuwa ne bayan da Isra'ila ta zargi cewa, ma'aikatan hukumar da dama ne aka gano suna da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Octoban bara. Gwamnatin Berlin ta ce ta dakatar da dukkannin wani tallafi da ta ke bayar wa ga hukumar har zuwa lokacin da za a kamalla bincike. Shugaban hukumar ta UNRWA, Philippe Lazzarini ya ce zargin ya shafi wasu takaitattaun ma'aikata ne, kana ya ce za a hukunta duk wanda aka kama da hannu cikin harin.
Sai dai ya nuna kaduwarsa kan dakatar da tallafin yana mai cewa,Falasdinawa a Zirin Gaza ba su cancanci wannan hukuncin na bai daya ba. A baya-bayan nan, dangantaka tsakanin Isra'ila da UNRWA na tsami sakamakon zargin da hukumar ke yiwa Isra'ilar na kai hari kan mafakar da ta ke bai wa 'yan gudun hijira.