1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na son Isra'ila ta kiyaye hakin dan'Adam

July 4, 2023

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bukaci Isra'ila ta kiyaye hakkin dan'Adam a yayin da aka shiga kwana na biyu na samamen da ta kaddamar a birnin Jenin na yammacin kogin Jordan.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock tana ganawa da manema labaraig
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock tana ganawa da manema labaraiHoto: Thomas Koehler/photothek/picture alliance

A cikin wata sanarwa, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, ta bayyana matukar damuwa kan abin da ke furuwa a yankin Falasdinawa, da ma asarar rayukan mutane 10.

Har wa yau Annalena Baerbock ta kuma yi tir da harin kunar bakin wake da aka kai wa birnin Tel-Aviv na Isra'ila a wannan Talatar, sai dai kuma ta ce duk da yake Isra'ilar na da 'yancin kare kanta daga duk wata tsokanar Falasdinawa, to amma ya kamata ta kiyaye hakkin fararen hula.    

Babbar jami'ar diflomasiyyar ta Jamus, ta bukaci duk wasu masu ruwa da tsaki a yankin da su yayyafa wa wutar rikin ruwan sanyi.