1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta kaddamar da makamun kare sararin samaniya

Suleiman Babayo LMJ
December 3, 2025

Jamus ta fara aiki da makamai masu kare sararin samaniyar kasar, sakamakon barazana da kasashenTurai ke fuskanta bayan yakin da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine.

Makaman kare sararin samaniyar Jamus
Makaman kare sararin samaniyar JamusHoto: Sebastian Gollnow/dpa/picture alliance

Kasar Jamus ta kaddamar da aiki da makamun kariya daga harin makamai masu linzami, wanda aka gina da zai iya cafke duk wani makamun da aka harba mai tafiya tsakanin kasa da kasa.

Dalilan karfafa tsaron Jamus

Haka yana cikin matakan da Jamus ke dauka tun bayan hare-haren da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine, tare da barazanar da Rasha ke yi ga sauran kasashen Turai.

Boris Pistorius ministan tsaron JamusHoto: Elisa Schu/dpa/picture alliance

Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius ya jaddada cewa wanna kariya daga makamai masu linzami na cikin matakan kare kasar da ake dauka. Kuma wannan zai karfafa tsaro tsakanin kasashen kungiyar tsaron NATO.

Kasashe da dama na duniya suna muradin sayen wannan makamun kariya na Jamus, wanda Isra'ila ta yi amfani da shi lokacin da makamun ya taimaka wajen kare wasu hare-haren Iran lokacin fafatawa tsakanin kasashen biyu na Isra'ila da Iran.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW