1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta fuskanci kutsen jirage marasa matuka fiye da 1,000

December 22, 2025

Hukumomin Jamus suka ce babu hujjar da ta tabbatar da cewa kutsen na 2025 daga Rasha ne.

Hukumomin Jamus suka ce babu hujjar da ta tabbatar da cewa kutsen na 2025 daga Rasha ne
Hukumomin Jamus suka ce babu hujjar da ta tabbatar da cewa kutsen na 2025 daga Rasha neHoto: Cover-Images/IMAGO

'Yan sanda a Jamus suka ce sun samu rahotannin kutsen jirage marasa matuka sama da 1,000 a shekarar 2025.

'Yan sandan sun shaida wa jaridar Bild cewa suna tattara cikakken rahoto a matakin kasa game da wadannan lamura tun a farkon shekara, inda ake amfani da dukkan bayanan da ake da su tare da hadin gwiwar rundunar sojojin Jamus.

Berlin na zargin Moscow da yi wa nahiyar Turai barazana

Suka ce mafi yawan jiragen da suka yi kutse sun yi ne a wuraren soji da filayen jiragen sama, sai kuma wasu muhimman wurare kamar kamfanonin tsaro da tashoshin jiragen ruwa.

'Yan sandan sun kara da cewa ba za a iya tabbatar da cewa kutsen daga Rasha bane tunda babu cikakkiyar hujja da ke tabbatar da hakan.

Jamus ta yi allawadai da harin Rasha kan Poland

A ranar Laraba, Jamus ta kaddamar da Cibiyar Hadin Gwiwar Kare Sararin Samaniya a birnin Berlin, domin inganta ganowa da kuma dakile kutsen jirage marasa matuka a kasar nan gaba.