1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta gargadi Rasha kan Ukraine

February 14, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci Rasha ta sakar wa Ukraine mara tare da gargadin cewa zata fuskanci hukunci mai tsauri idan har ta mamaye makwabciyarta.

Olaf Scholz | Shugaban gwamnatin Jamus
Hoto: Michele Tantussi/Getty Images Europe/Pool/dpa/picture alliance/

Scholz ya ce idan har Rasha ta kai farmakin soji kan Ukraine wanda yake barazana ga 'yancin kan yakinta da kuma ikonta, babu makawa akwai takunkumai masu tsauri da aka tanadar a tsanake wanda kuma za a aiwatar da su ne a nan take tare da hadin kan kasashen kungiyar tsaro ta NATO da kuma na Turai.


Kalaman shugaban gwamnatin na zuwa ne yayin da yake shirin kai ziyara birnin Kyiv fadar gwamnatin Ukraine da kuma Moscow na kasar Rasha don tattaunawa kan takun-sakar da ke tsakanin kasashen.


A ranar Juma'a data gabata ce dai Jaridar Der Spiegel ta ruwaito cewa akwai yiwuwar Rasha wadda ta girke dubban sojojii a iyakarta da Ukraine ta iya mamaye kasar a ranar Laraba mai zuwa, sai dai kuma jami'an Amirka sun ce babu tabbacin sahihin rana, zargin mamayar da Rashar ta musanta tun a baya.