1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta gargadi 'yan gudun hijirar Siriya

Zulaiha Abubakar
August 19, 2019

Ministan harkokin cikin gida na Jamus Horst Seehofer ya gargadi 'yan gudun hijira daga Siriya game da yawan tafiya hutu kasar su.

Horst Seehofer
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Ministan ya kuma kara da cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan Jamus ta shirya don fara janye damar zaman gudun hijira ga duk wanda aka samu da yawan zuwa hutu Siriya, duk kuwa da cewar bai bayyana adadin mutane nawa binciken ma'aikatar ya samu da wannan laifi ba.

Mahukuntan Jamus basu da ikon mayar da 'yan gudun hijirar kasar sakamakon rashin tsaro a yankin na gabas ta tsakiya. Sai dai wa'adin haramcin mayar da 'yan gudun hijirar zai kare a karshen shekarar bana kodayake akwai damar karin lokaci.