1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Jamus ta gargadi 'yan kasarta a kan zuwa Bangladesh

Zainab Mohammed Abubakar
July 22, 2024

Matakin na zuwa ne bayan dakatar da zanga-zangar adawa da gwamnati da ya rikide zuwa tarzoma, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutane 163 daura da daruruwa da suka jikkata.

Bangladesch  Ausgangssperre nach Protest von Studenten gegen Quotenregelung
Hoto: Mohammad Ponir Hossain/REUTERS

Abin da ya fara da zanga-zangar nuna adawa da yadda aka sanya siyasa a kan kudaden shigar da gwamnati ke nema, ya rikide zuwa munanan tashe-tashen hankula na zamanin mulkin  Firaminista Sheikh Hasina.

An kafa dokar ta-baci, kana sojoji suna sintiri a biranen kasar ta Kudancin Asiya, yayin da matakin toshe hanyoyin sadarwa na Internet a fadin kasar tun ranar Alhamis ya takaita yaduwar bayanai.

A wannan Litinin (20.07.2024) dai titunan Dhaka babban birnin kasar ta Bangladesh sun kasance cikin kwanciyar hankali , kuma babban hafsan sojojin ya ce "an shawo kan matsalar doka da oda" tun lokacin da aka tura sojoji.

Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta shawarci 'yan kasar da su guji zuwa kasar ta Bangladesh.