Jamus ta halarta wuy-wuy
August 16, 2023
Matakin na gwamnatin Jamus wani kari ne bisa karbuwar da kasashen duniya ke yi na aminta da tabar Wuy-Wuy, inda masana ke cewa ana matukar bukatar ganyen na wuy-wuy don hada magunguna. Don hakama dai a martaninsa 'yan sa'o'i bayan da majalisar ministocin suka amince da halarta tabar ta wuy-wuy, Karl Lauterbach ministan kiwon lafiyan ya kwatanta matakin a matsayin wani babban sauyi a fannin kiwon lafiyan kasar. Shi kuwa shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce yana fatan dokar halartawan za ta kare masu zukar wuy-wuy wajen shan gurbataccen ganye, kuma zai rage wa fannin shari'a tulin aiki da ya shafi karaki kan masu zukar wuy-wuy. Dokar dai ta amince wa balagaggun 'yan kasar su iya mallakar gram 25 na tabar ba tare da gudun saba ka'ida ba.