Jamus ta samu gurbi a kwamitin sulhu
January 1, 2019Talla
Heiko Maas ya kara da cewar Jamus ta shirya tsaf don fuskantar kalubalen da ke gabanta.Taraiyar Jamus dai ta zamo daya daga cikin kasashe 10 da suka sami wakilcin karba karba a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar bayan kasashen Faransa da Rasha da Birtaniya da Chaina da Amirka wadanda ke da kujerun dindindin a kwamitin sulhun. Kare mata da yara kanana a yankunan da ake yaki da batun muhalli da kuma tsaron lafiyar ma'akatan agaji a kasashen dake rikici na daga cikin kudirorin kasar ta Jamus a kwamitin tsulhun Majalisar Dinkin Duniyar.