Yunkurin Jamus na mayar da 'yan Siriya a gida na nan daram
March 31, 2026
Ministan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya yi karin haske game da batun da firaministan kasar Friedrich Merz ya gabatar na cewa kusan kashi 80 cikin 100 na 'yan kasar Siriya masu gudun hijira za su koma kasarsu ta sali.
Merz da Sharaa sun amince da aiki tare kan 'yan hijira
A cewar Johann Wadephul, gwamnati na ci gaba da duba batun tsaro da yanayin da ke cikin a Syriya kafin daukar duk wani matakin, tare da nanata cewar duk wani yunkuri zai kasance ne bisa ka'ida ta kare hakkin bil'adama da tafarkin kasa da kasa.
Gwamnatin Jamus ta ce a shirye take da ta kori duk wasu 'yan kasashen ketare da ba su cika ka'idar zama a kasar ba, a yayin wata ziyarar aikin da ya kai a Ukraine, ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul din, ya ce gwamnatin Jamus na da cikakkiyar anniya korar dukkan mutanen da ba su cika dokokin bakunci a Jamus ba.
Me yasa aka haramta sayar da barasa a Siriya?
Johann Wadephul ya ce babban burin taron da aka yi a baya kan kasar Siriya, shi ne a gina ta domin ta zama kasa mai tsaro da damarmmaki irin na tattalin arziki, domin hakan zai karfafa wa ’yan kasar komawa gida tare don taimaka wa ci gaban kasarsu.