1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta kaddamar da kamfanin samar da magunguna a Rwanda

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 18, 2023

Magungunan da za a samar, sun hada da na rigakafin cutar Covid-19 da zazzabin cizon sauro wato maleriya da kuma na tarin fuka

Hoto: Florian Gaertner/photothek/picture alliance

Jamus ta ce kamfanin samar da magunguna na BioNtech da ta kaddamar a birnin Kigali na kasar Rwanda, wata alama ce ta kyakkyawar alaka da kuma hadin kai da ke tsakanin nahiyar Afirka da Turai.

karin bayani:Shari'ar kisan kiyashin Ruwanda a Paris

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, wadda ke ziyarar aiki yanzu haka a Rwanda, ta ce duniya ta gaza matuka wajen samar da magungunan rigakafi ga kowa da kowa a duk lokacin da wata annobar cuta ta barke, wannan dalili ne ya zaburar da Jamus wajen ganin da samar da mafita ga al'ummar Afirka da ma duniya.

Karin bayni:Rwanda ta fara rage cunkoson gidajen yari

Daga cikin magungunan da za a samar a kamfanin na birnin Kigali, sun hada da na rigakafin cutar Covid-19 da zazzabin cizon sauro wato maleriya da kuma na tarin fuka.