1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da sansanin sojin Jamus a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
November 12, 2018

Jamus na a jerin manyan kasashen duniya da ke agazawa Nijar a kokarin da take na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar da kuma yankin Sahel.

Verteidigungsministerin  von der Leyen im Niger
Hoto: picture-alliance/M.Kappeler

A Jamhuriyar Nijar ministar tsaron kasar Jamus Ursula von der Leyen ta kammala wata ziyarar aiki a kasar tare da kaddamar da sansanin sojan kasar Jamus a birnin Yamai da kuma baiwa kasar tallafi na wasu motocin yaki da na dakon kaya na makudan kudade domin agazawa Nijar a kokarin da take na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar da kuma yankin Sahel.

Wannan dai shi ne karo na uku ministar tsaron ta Jamus ke ziyarar Nijar a hukumce da zummar ganawa ta hakika da sojan kasar Jamus da ke jibge a Nijar a wani mataki na shirin ko ta kwana da kawo dauki ga wasu tarin askarawan kasar da ke aikin dafa wa zaman lafiya karkashin rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta Minusma da ke Mali.

Sai dai ko baya ga ganawar ta ido da ido tsakanin Ursula von der Leyen da sojojin kasar da ke birnin Yamai, wani babban makasudin ziyararta a Nijar din shi ne na kaddamar da sansanin sojan Jamus din a hukumce da yau shekaru biyu kenan da rabi da gwamnatocin kasashen biyu suka kulla yarjejeniya kafawa da ke baiwa sojan kasar tarayyar Jamus damar samun mafaka a Nijar a yakin da suke yi da yan ta'adda a Mali da yankin Sahel.

Hulda tsakanin Jamus da Nijar ta inganta

Minista von der Leyen ta bayyana irin yadda Jamus ke jinjinawa matsayin huldarta da kasar Nijar inda tace Jamus na godiya da wannan goyon bayan da kasar take samu daga abokiyar dasawarta Nijar musamman ma wajen kafa wannan sansani da ke a matsayin mafaka ta sojan kasar Jamus.

Ursula von der Leyen da takwaran aikinta na Nijar Kalla Moutari Hoto: picture-alliance/M.Kappeler

"Nijar da Tarayyar Jamus dai dukannin kasashen biyu sun hadu ne a matsaya daya ta yaki da ta'addanci a yankin Sahel domin samun cikakken zaman lafiya da ma wani yanki na Sahel mai cike da tsaro da kwanciyar hankali, wanda zai baiwa 'yan kasashen damar sakewa a cikin yanayi na tsaro domin kuwa ababen batanci kamar ta'addanci, sumogar makamai da miyagun kwayoyio da na bil Adam na gallazawa yankin baki daya, kana kuma ana dandana illolinsu har a Tarayyar Turai. Saboda hakan tare gaba dayanmu za mu fuskanci wannan kalubalai, ina nufin a nan Nijar da Jamus da kasar Faransa da sauran wasu tarin kasashe na Tarayyar Turai."

Bisa wannan dangantaka ce ma dai kasar Jamus ta tallafawa Nijar da makudan kudade a bara wajen gina makarantar horas da hafsoshin soja a yankin Agadez da kudi fiye da Sefa miliyan dubu uku 3, baya ga wasu tarin motoci da babura da kayan aikin soja da kasar ta baiwa Nijar a matsayin tallafi don tabbatar da tsaro da yaki da tabi'ar safarar bil Adama.

Kayan aiki don samar da zaman lafiya

Duk da hakan ma dai a wannan karon kasar ta Jamus ta baiwa Nijar wasu hamshakan motoci akalla 53 domin tabbatar da tsaro tare da horas da direbobinsu sanin makamar aiki, matakin da ministan tsaron Nijar Malam Kalla Moutari ya ce abin yabawa ne matuka.

Wasu daga cikin motocin da Jamus ta bawa sojin NijarHoto: picture-alliance/M.Kappeler

"Idan muna son kwasar sojojinmu don kai su wani wurin a cikin gaggawa sai mu kwashesu da wannan motocin, idan kuwa na jirage ne muna da hulda da Jamus da ke ba mu damar daukar jirage da sauransu. Huldarmu hulda ce da ke iya taimaka mana sosai da kuma ke neman inda muke bukatar tallafi don su kawo mana ta su gudunmawa."

An dai kaddamar da sansanin sojan na Jamus da ke Yamai a hukumce albarkacin wannan ziyara ta ministar tsaron Ursula von der Leyen shekaru biyu da rabi bayan kaddamar da shi a rubuce. Sansanin dai a cewar ministan tsaron Nijar Kalla Moutari, a hukumce Nijar za ta ci amfaninsa matuka.

"Yau muna da mutanen da muke iya saukewa a nan muna da kuma jiragen da ke iya tashi da sauka a nan ba tare da wani matsatsi ba. Muna ganin ababe na karuwa da yawa wanda wannan huldar tsakaninmu da Jamus ke kawowa."

Ministar dai ta shafe tsawon daren Lahadi a cikin sansanin sojan kasar ta Jamus tare da tattaunawa ta keke da keke da sojan kasar bisa wasu fannoni da dama kan ta wuce zuwa kasar Mali a ranar Litinin.