1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta kammala janye sojojinta daga kasar Nijar

Gazali Abdou Tasawa
August 30, 2024

A wannan Juma'a ce sojojin Jamus da ke kasar Nijar suka kammala ficewa baki daya tare da kayansu.

Sojojin Jamus sun kammala janyewa daga Nijar
Sojojin Jamus sun kammala janyewa daga NijarHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Sojojin na Jamus sun bar wa takwarorinsu na kasar ta Nijar gadon wasu kayan aiki da suka hada da motoci da da wasu na'ororin aiki. To amma a loakcin da wasu ‘yan Nijar din ke yaba wa da yadda aka rabu lami lafiya da Jamusawan wasu na nuna damuwa kan asarar da Nijar za ta yi a cikin lamarin. 

Karin Bayani: Jamus za ta kammala janye sojojinta a Nijar

Rattaba hannu kan yarjejeniyar kammala janyewar sojojin Jamus daga NIjarHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Rukunin karshe na sojojin na Jamus ya fice da kayansa zuwa gida kamar yadda kasar ta Jamus ta cimma yarjejeniya da hukumomin mulkin sojin Nijar da suka bukaci su fice daga kasar kamar yadda ta kasance ga sojojin Faransa da na Amirka a watannin baya.

Kafi tashin jiragen sojojin Jamus din dai an gudanar da biki karkashin jagorancin Colonel Major Mahamane Sani Kiaou shugaban rundunar soji kasa na Nijar da kuma Kanal Karsten Struss na rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr inda suka fitar da sanarwar hadin gwiwa ta tabbatar a hakumance da kawo karshen aikin kwashe sojojin Jamus din wanda aka soma tun a ranar 19 ga wannan watan Agusta 2024.

Karin Bayani: Nijar: Makomar sojojin Jamus a Sahel

Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane TianiHoto: Balima Boureima/Reuters

"Ma'aikatar tsaron Nijar da takwararta ta Jamus na farin cikin sanar da kawo karshen  ficewar sojojin Jamus daga Nijar tare da rufe sansaninsu da ke a babban filin jirgin saman sojojin Nijar da ke Yamai. Sojojin Jamus din sun fice daga wannan sansani ne a karkashin matakin da Jamus ta dauka na janye sojojinta daga Nijar. Kuma aikin ficewar tasu ya Wakana a cikin tsari da fahimtar juna. Sai dai wannan mataki na janye sojojin ba ya nufi kawo karshen yarjejeniyar tsaron da ta hada Nijar da Jamus. Kasashen biyu sun yanke shawarar ci gaba da huldarsu a fannin harkokin soja"

Manyan jiragen dakon kaya sun yi sawu biyar wajen kwashe sojojin kasar ta Jamus guda 60 da kuma ton 146 na kayan aikinsu. Kuma tuni wasu kungiyoyin fafutika na kasar Nijar suka soma bayyana mabanbantan ra'ayoyi a game da ficewar sojojin Jamus din daga Nijar:

Karin Bayani:Tababa game da zaman sojojin Jamus a Sahel

Wasu yan Nijar yayin gangamin nuna goyon baya ga Janar Abdourahamane TianiHoto: AFP/Getty Images

"Lallai yau Jamus ta bar Nijar. Kuma haka ya kamata a yi. Da ma mun san sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba. Kuma da ma Faransa ce ta kawo mana duk wannan kwamacalar. To bayan Jamus akwai sauran Turawa da suke nan. To kafin mu waiwayo su, su ma muna kiransu salin-alin su bar mana kasarmu. Saboda Nijar din yanzu ba ta da ba ce"

To mun gode Allah da muka rabu da su lami-lafiya. Amma muna ganin wannan tafiya ta sojojin Jamus tamkar wata babbar asara ce ga kasa ga kuma sojojin Nijar saboda namijin kokarin da su sojojin Jamus din suke yi na ba wa sojojin horo da kawo masu gudunmawa 

Daga karshe sojojin kasar ta Jamus wadanda adadinsu ya kai kimanin 120 sun bar wa rundunar sojin Nijar gadon wasu kayayyaki da suka hada da motoci 26 da manyan injinan lantarki da na'urorin tace ruwan sha da tarin dakunan tafi da gidanka da suka yi rayuwa a cikinsu da dai sauran kananan na'urorin aikin.