Jamus ta karɓi 'yan gudun hijira daga Libiya
September 4, 2012Hukumomi a ƙasar Jamus sun yi marhabin lale da rukunin farko daya ƙunshi 'yan gudun hijirar Libiya, a matsayin wani bangare na shirin sake tsugunar da jama'ar na Majalisar Ɗinkin Duniya. 'Yan gudun hijirar da adadin su yakai 195, waɗanda suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Hannover da ke tarayyar Jamus a wannan Litinin, sun kwashe tsawon shekara ɗaya suna sansanin 'yan gudun hijirar da ke ƙasar Tunisiya. Galibin su kuma sun rasa matsugunan su yayin rikicin ƙasar ta libiya. Sai dai gabannin jigilar su zuwa Jamus, sun samu horon tsawon makonni biyu game da tsarin harshe da kuma na al'adun Jamusawa a ƙasar ta Tunisiya. Hakanan za su ɗauki tsawon makonni biyu a wani sansanin da ke nan Jamus domin sanin irin kalubalen rayuwar da ke gaban su. Bayan haka ne kuma za'a rarraba 'yan gudun hijirar zuwa wasu jihohin Jamus daban daban.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar