1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta kara yawan takardun biza ga 'yan Indiya

October 25, 2024

Jamus ta cimma sabuwar yarjejeniya da Indiya wadda ta jibanci kara yawan kwararrun ma'aikata Indiyawa da ke zuwa aiki kasar.

Deutsch-indische Regierungskonsultationen in Neu Delhi
Hoto: Marvin Ibo Güngör/dpa/picture alliance

Jamus ta yi alkawarin kara yawan kwararrun idiyawan da take ke bai wa izinin yin aiki a kasar, a yayin ganawar da shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz ya yi da firaministan Indiya Narendra Modi a wannan Juma'a a birnin New Delhi.

Karin bayani: Jamus da Indiya sun cimma yajejeniyar karfafa alaka

Shugaban gwamnatin na Jamus ya ce daga yanzu za a kara yawan takardun biza da ake bai wa indiyawa daga 20,000 zuwa 90,000 a duk shekara, yana mai cewa Jamus kofarta a bude ta ke ga kwararrun ma'aikata. Kazalika Jamus din ta yi alkawarin sassauta matakan da ake bi don samun takardun biza ga 'yan indiya musamman ma ga wadanda suke da kwarewa a fannin aiki.

Daga nasa bangare Narendara Modi ya yaba da wannan yarjejeniya wacce ya bayyana a matsayin mai cike da alfanu ga tattalin arzikin kasashen biyu.