1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta karbi jagorancin kungiyar G7

January 1, 2022

Ministan kudi na Jamus Christian Lindner ya ce ya yin jagorancinta a kungiyar kasashe G7, Jamus za ta yi amfani da damar hakan wajen farfado da tattalin arzikin duniya.

Das Logo der deutschen G7-Präsidentschaft 2022
Hoto: Michael Sohn/AP Photo/picture alliance

A sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, Lindner ya ce ya zama wajibi a kawo karshen annobar corona da kuma karfafa matakan kare muhalli.

A matsayinsa na ministan kudi, ya na fatan ganawarsa da suran ministocin kudi da kuma gwamnonin manyan bakunan kasashe ta samar da daidaito a batun sauyin yanayi ba a Jamus kadai ba, har tsakanin kasashen kungiyar ta G7.

A ranar 1 ga watan Janairun nan ta shekarar 2022 ce Jamus ta karbi jagorancin karba-karba na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya wato G7.