SiyasaJamus
Jamus ta kori Jami'ar diflomasiyyar Rasha
January 22, 2026
Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta kira Jakadan Rasha a Jamus inda ta shaida masa korar wata Jami'ar diflomasiyyar Rasha kan zargin leken asirin kasa.
Korar Jami'ar ta biyo bayan kama wata mata ne da hukumomin Jamus suka yi wadda suke zargi da mika bayanan sirri kan yakin Ukraine.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin sada zumunta, ma'aikatar harkokin wajen ta ce gwamnati ba za ta lamunci leken asiri a cikin kasar Jamus ba musamman ga mai rike da matsayin jami'in diflomasiyya.
A waje guda kuma ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul ya ce ba a bukatar jami'ar a cikin Jamus kuma an umarci ta gaggauta barin kasar ba tare da jinkiri ba.