1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jamus ta mayar da mutum na farko Siriya

Suleiman Babayo MAB
December 23, 2025

Jamus ta mayar da mutum na farko kasar Siriya tun lokacin da kasar ta shiga yakin basasa. Haka na zuwa lokacin da ake samun tashe-tashen hankula a kasar ta Siriya duk da kwarya-kwaryar zaman lafiya da ake gani.

Birnin Aleppo na Siriya
Birnin Aleppo na SiriyaHoto: SANA/dpa/picture alliance

A karon farko tun shekara ta 2011 da kasar Siriya ta fada cikin yakin basasa, kasar Jamus ta mayar da mutum na farko zuwa kasar ta Siriya wanda ya nemi mafaka. Mutumin dan Siriya, a baya an same da aikata manyan laifuka a Jamus, kuma yanzu haka an mayar da shi zuwa birnin Damascus na kasar ta Siriya, inda aka mika shi ga hukumomin kasar.

Siriya tana sake rikicewa

Wannan na zuwa lokacin da mutane uku suka halaka a wani sabon rikicin da ya barke a birnin Aleppo na arewacin kasar Siriya tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai masu goyon bayan gwamnati da kuma na Kurdawa.

Rikicin ya janyo wasu kusan mutane 20 sun jikata, inda gwamnatin ta Siriya ta yi zargi an kai harin kan mayakan da ke karkashin ikonta a wajen da suke binciken ababen hawa.