Jamus taki a sassauta bashin Girka
July 7, 2015 Ministan harkokin tattalin arzikin Jamus ya bayyana a wata hira da 'yan jarida ranar Talatan nan cewar akwai yiwuwar tattaunawa kan shirin rage wa ƙasar Girka bashin da ake binta abu ne da ba za a iya hassashe ba har sai mahukuntan na birnin Athens sun gabatar da sauye-sauye da aka gabatar musu.Sigmar Gabriel ya faɗa wa mujallar Stern da ke yaɗa labaranta a shafin intanet cewa, an buƙaci kawai a rage bashin da ake bin ƙasar Girka ba tare da ta gudanar da sauye-sauye ba a fannita na tattalain arziki abu ne da ba zai haifar da da mai idanu ba.
Ƙasar ta Jamus dai ta tsaya kai da fata kan kudirinta na kin amincewa da neman a gudanar da kwaskwarima kan rage wancan bashi.
Shugabanni daga ƙasashen na EU sun gargadi Firaminista Alexis Tsipras na Girka da ya gabatar da sabon shiri da ƙasar ke yi kan bashin da ake binta a wajen taron da ake yi a ranar Talatan nan ko kuma kasar ta iya fiskantar ficewa daga ƙasashen da ke amfani da kuɗin bai daya na Euro, bayan da al'ummar ƙasar ta Girka suka zaɓi kaɗa a ƙara musu wani karin matakai na tsuke bakin aljihu.