Jamus ta nuna adawa da huldar EU a Turkiya
August 29, 2017Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi watsi da aniyar shigar daTurkiya a cikin tsarin aikin kwastam ko na kasuwancin na bay daya na kasashen Turai matsawar ba ta ta nuna wani ci gaba ba a fannin kiyaye hakkin dan Adam ba.
"Merkel ta ce a halin yanzu ci gaban Turkiya na tafiya a baibai ne, ba za mu ce mun yanke kauna ba da ita. amma a yanzu dangane da batun hulda da ita a fannin tattalin arziki ba ni ga za mu iya ba da izinin a soma tattaunawa da ita matsawar babu sauyi daga halin da ake ciki a kasar a yanzu"
Tun a shekara ta 2005 ne dai kungiyar EU ta soma tattaunawa da Turkiya kan batun shigarta a cikin kungiyar , sai dai lamarin ke tafiyar hawainiya a bisa zargin da kasashen Turan ke yi wa Turkiyar na kin mutunta hakkin dan Adam.