Corona: Rufe kan iyakonin Jamus da wasu kasashe
March 15, 2020Talla
Matakin rufe iyakokin da hukumomin Jamus suka yi zai shafi Faransa da Ostriya da Swizland wadanda dukkansu ke fama da annobar coronavirus.
Baya ga batun hana yaduwar cutar ta Coronavirus ga 'yan kasar, a daya bangaren Jamus na zargin 'yan kasashen da kwarara a cikin kasar suna sayen kayan cimaka da ababen more rayuwa.
Sai dai bayanai sun ce matakin ba zai shafi motocin dakon kaya ba sannan kuma zai daga kafa ga wasu kwarorin ma'aikata na kan iyakokin.
Kawo yanzu mutane takwas ne suka rasa rayukansu daga cikin fiye da dubu uku da suka kamu da cutar ta Covid-19 a nan Jamus.