1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta sake jan hankali a kan cutar corona

April 15, 2021

Gwamnati da likitoci a Jamus, na ci gaba da jan hankali jama'a a kan girmama ka'idodjin corona ta yadda za a iya kauce wa shiga mataki na uku da ke nuna ta'azzarar cutar.

Jens Spahn Bundesgesundheitsminister Coronavirus Pressekonferenz
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A jawabin da ya gabatar a wannan Alhamis game da wannan bukata a birnin Berlin, ministan lafiya Jens Spahn, ya ce babu ranar da ba ta da muhimmanci a matsayin da ake kai na yaki da wannan annoba.

Ya ce har yanzu adadin wadanda ke kamuwa da cutar na ci gaba da karuwa. Halin da ake ciki a sassan ba da kulawa ta musamman ga masu wannan cuta sai gaba-gaba yake yi. Don haka wannan yanayi, ya sanya dole ne a saurari abin da likitoci a wadannan wuraren ke cewa.

Sama da mutum dubu 29 ne dai hukumomi ke cewa suka kamu da coronar a Jamus cikin sa'o'i 24 da suka gabata, abin da ya doshi mutum dubu 37 da aka gani a lokacin da annobar ta fi muni a baya.