1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta shirya bai wa Siriya tallafin kudade

December 12, 2024

Jamus ta sanar da ware wasu mkudan miliyoyi na Euro domin tallafa wa Siriya bayan rugujewar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad a karshen mako. Siriya dai a yanzu na bukatar 'ya'yanta da ke ketare su koma gida.

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena BaerbockHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Gwamnatin kasar Jamus ta ce za ta samar da karin kudaden da yawan su zai kai euro miliyan takwas, kwatankwacin dala miliyan takwas din da dubu 400 domin taimaka wa Siriya ta fuskar agaji.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, ta ce lokaci ne da Siriya ke hangen sabon fata na samun daidaituwa.

Baerbock ta kuma ce za atsara shirin mayar da 'yan Siryia kasarsu da kawaye na nahiyar Turai da ma Majalisar Dinkin Duniya.

Sannan kuma ta yi kira ga kasashen Isra'ila da Turkiyya da kada su kawo cikas ga shirin kafa sabuwar gwamnati a Siriya bayan kawo karshen ta hambararren Shugaba Bashar al-Assad.

A halin yanzu dai, Firaminista mai rikon kwaryar gwamnatin Siriya, Mohammed al-Bashir ya yi kira ga 'yan kasar da suka tsere zuwa wasu yankuna na duniya da su koma gida, yana mai cewa kasar ta gano daraja da karfinta.