1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ukraine:Jamus ta nufi Qatar neman iskar gas

March 19, 2022

Jamus dai ta tsunduma neman iskar gas a kasashen duniya biyo bayan kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine, lamarin da ke barazana ga alakar diflomasiyya ciki har da sayen makamashin iskar gas da Jamus din ke yi daga Rasha.

Bundeswirtschaftsminister Habeck in Katar
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Ministan kula da bunkasar tattalin arziki a Jamus  Robert Habeck na kan hanyarsa ta zuwa kasar Qatar, a wani bangare na kokarin da Jamus ke yi na fadada hanyoyin da take samun iskar gas. Ziyarar ta Habeck a kasar Qatar, babbar mai arzikin iskar gas na zuwa ne bayan irin ta da ministan ya kai kasar Norway a cikin wannan makon. 

Rikicin Ukraine dai ya tilasta wa Jamus da Rasha dakatar da shirin shimfida bututun iskar gas na Nord Stream 2 daga Rashan zuwa Jamus. 

Tawagar ministan kula da bunkasar tattalin arziki na Jamus din dai na sa ran ganawa da 'yan kasuwar Qatar da niyyar fitowa da hanyoyin cinikayyar makamashin da kasashen Turai ke neman sa ruwa jallo a wannan lokaci da suke zaman doya da manja da kasar Rasha.