1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ukraine ta samu taimakon dakile barazanar Rasha

Ramatu Garba Baba
April 19, 2023

Jamus ta mika wa Ukraine wasu sabbin makamai da ke dauke da na'urori masu iya dakile duk wasu hare-hare da makamai masu linzami daga abokiyar fadanta Rasha.

Deutschland liefert Marder-Panzer und Patriot-System an Ukraine
Hoto: Axel Heimken/dpa/picture alliance

Jamus ta sanar da tura wa Ukraine wasu sabbin makamai na musanman domin taimaka mata kare kanta daga duk wasu hare-hare da Rasha za ta kai mata da makamai masu linzami da ma wadanda ke iya sarrafa kansu.

Amirka da Jamus na daga cikin kasashen duniya da suka amince da bai wa gwamnatin Kyiv tallafin irin wadannan makaman a kokarin ganin ta iya dakile duk wani yunkurin daga rundunar sojin Rasha na kai wa kasar hare-haren da ke barazana ga rayuwar fararen hula da dukiyarsu.