Jamus ta tallafa wa 'yan Siriya da kudi
March 14, 2019Jamus ta sanar da tallafin kudi miliyan dubu daya da 440 na Euro ga 'yan gudun hijirar Siriya, yayin da Kungiyar Tarayyar Turai za ta bayar da miliyan dubu biyu 2 don cetosu daga mummunan halin da suka shiga. Wakilan kasashe da hukumomin na Turai su yi wannan alkawari ne a lokacin taron ministoci na taron bada tallafi ga Siriya da ke gudana a birnin Brussels na Beljiyam. Ita ma gwamnatin Birtaniya ta kudiri aniyar bayar da kwatankwacin Euro miliyan 464 ga Siriya, yayin da Ostiryia za ta bayar da miliyan 9 na Euro.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta bukatar miliyan dubu biyar da 500 don taimaka wa 'yan Siriya miliyan biyar da dubu 600 da ke tsugune a Turkiya da Lebanon da Jordan, da Iraki da kuma Masar. Sannan tana bukatar dala miliyan dubu uku da 300 ga 'yan Siriya da gudun hijira a kasarsu. A makamancin irin wannan taro da ya gudana a shekarar da ta gabata dai, yawan kudin da MDD ta samu don taimaka wa 'yan gudun hijirar Siriya ya yi kasa da abin da ta bukata tun da farko.