Jamus ta tsawaita dokar kulle
January 20, 2021Shugabar gwamnatin Jamsu Angela Merkel da shugabanin jihohi 16 sun cimma matsayar ce a wani mataki na dakile yaduwar annobar da ke kara yaduwa a kasar.
Kazalika, shugabannin sun ce ya zama wajibi dukan fasinjoji su ci-gaba da sanya takunkumin fuska kamar yadda aka saba a ababen hawa na haya, da cikin shagunan siyar da kayayyakin amfanin yau da kullum. Ma'aikata kuma za su ci-gaba da yin aiki daga gida a inda ake da bukatar hakan.
Dama dai tuni a watan Nuwanba bara ne kasar ta rufe makarantu da sauran shaguna da gidajen cin abinci da na siyar da barasa da kuma haramta haduwa mutane da dama a wuri guda.
Adadin masu dauke da cutar corona a Jamus sun karu inda a halin yanzu mutum fiye da miliyan 2 ne suka dauke da ita a kasar yayin da mutum fiye da dubu 47 suka kwanta dama a cewar cibiyar Robert Koch.